Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 9 sun mutu sakamakon harin 'yan bindiga a tsakiyar Najeriya
2019-08-19 15:40:16        cri

Hukumar 'yan sandan jahar Benue dake shiyyar tsakiyar Najeriya ta ce mutane ne 9 aka hallaka a safiyar ranar Asabar a lokacin bikin binne mamaci a gundumar Tongov dake jihar.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar ta ce tuni jami'an suka fara bincike game da afkuwar lamarin, tare da bada tabbacin gurfanar da wadanda aka samu da hannu a laifin a gaban shari'a.

Ta yi kira ga jama'a da su taimakawa 'yan sanda da muhimman bayanan da za su taimaka musu wajen gano wadanda ke da hannu a aikata laifukan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China