![]() |
|
2019-11-21 10:38:46 cri |
Wata sanarwa da kakakin rundunar Ibikunle Daramola ya fitar, ta ce farmakin da rundunar ta kai, ya kuma yi sanadin mutuwar shugabannin kungiyar da dama.
Sanarwar ta ce an kai farmakin ne biyo bayan rahotannin sirri da rundunar ta samu cewa, shugabannin kungiyar sun hadu domin gudanar da taro a cibiyar, wadda kuma ta kasance wajen adana kayayyaki.
Sanarwar ta ce an kashe mayakan ne yayin da suke yunkurin tsere, kuma luguden wutan ya lalata wani bangare na cibiyar.
Ibikunle Daramola, ya kara da cewa, rundunar sojin saman za ta ci gaba da fatattakar ragowar mayakan kungiyar BH bisa hadin gwiwa da dakarun kasa. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China