Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Nijar ya kaddamar da taro don tattauna batun tsaro a yankin Sahel
2019-05-23 17:31:25        cri

A ranar yau ne 22 ga watan Mayu ne, shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou ya jagoranci wata ganawa ta musamman da manyan jami'an sojojin kasar Nijar da ma takwarorinsu na kasashen Faransa, Amurka, Jamus dana kuma wakilan kungiyar G5 Sahel. Haka kuma taron ya samu halartar jakadun wadannan kasashe dake Nijar, domin tattauna matsalar tsaro a yankin Sahel, musamman ma a Nijar inda a 'yan kwanakin baya bayan nan aka fuskanci hare-haren ta'addanci da na 'yan fashi da makami a yankunan Diffa, Tillabery da Maradi inda aka samu asarar rayuka da dama daga bangaren sojoji da ma fararen hula. Inda harin ta'addanci mafi tsanani ya faru a kauyen Tongo tongo dake yankin Tillabery inda dakarun Nijar na musammun suka cikin wani kwanton bauna na kungiyar 'yan ta'adda, lamarin da ya haddasa mutuwar sojojin Nijar guda 27 da jikkata 5 da yanzu haka ake jinyarsu a babban asibitin zamani cewa da Hopiral general de reference da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa dake birnin Yamai.

A karshen wannan haduwa, shugaban Nijar ya samu tabbaci da goyon bayan wadannan kasashe wajen yaki da mayakan Boko Haram da ma wasu kungiyoyi masu kaifin kishin Islama dake kan iyaka da kasar Mali, haka kuma kasashen sun kara bayyana niyyarsu ta kara samar da kayayyaki da kudade domin taimakawa kasar Nijar wacce ta mafi fama da hare-haren ta'addanci a baya bayan nan.

A nasa bangare, ministan tsaron kasar Nijar Kalla Moutari, ya bayyana cewa kasar Nijar ta sayi sabbin kayan yaki na zamani da za'a baiwa sojoji tare da jaddada cewa karshen Boko Haram ya kusa a Nijar da ma yankin G5-Sahel. (Maman Ada)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China