Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya yi kira da a karfafa kwarewa a ayyukan wanzar da zaman lafiya
2019-09-10 10:58:36        cri

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a dauki matakai na inganta kwarewa da sanin makamar aiki, yayin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya, matakin da a cewarsa zai inganta tasirin ayyukan.

Zhang Jun ya bayyana hakan ne, yayin zaman mahawarar kwamitin tsaron MDD game da ayyukan wanzar da zaman lafiya ko PKOs a takaice. Ya ce ya kamata kasashen duniya su kara nuna goyon baya ga hadakar dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashe daban daban ko TCCs, wadanda aikinsu ya hada da na ginin kasashen da suke aiki a cikin su.

Kaza lika su ma kasashen dake tura dakarun na TCCs, su tabbatar ana samar da horo da sanin makamar aiki, da kayayyakin gudanar da ayyukan da kuma kudade.

Mr. Zhang ya kara da cewa, ya kamata sakatariyar MDD ta kara dora muhimmanci ga batun tsaron lafiyar dakarun, da karfafa matakan kandagarkin fadawar su cikin garari, da ma sauran hidimomi da za su tabbatar da gudanar ayyukan su yadda ya kamata.

Kafin tsokacin na Mr. Zhang, shi ma sakataren sashen ayyukan wanzar da zaman lafiya na majalissar Jean-Pierre Lacroix, ya shaidawa kwamitin tsaron cewa, sashen lura da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD na daukar matakai na inganta ayyuka, ta yadda dakarun za su samu zarafin zirga-zirga, da gudanar da ayyukan su cikin managarcin tsari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China