Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan kasar Sin a Nijeriya ya rubuta rahoto a manyan jaridun Nijeriya
2020-02-11 11:26:05        cri
Jiya Litinin jaridar Leadership da sauran manyan jaridun kasar Nijeriya sun wallafa rahoton da Zhou Pingjian, jakadan kasar Sin da ke kasar Nijeriya ya rubuta, mai taken "yaki da annobar cutar numfashi ta hanyar kimiyya da hadin gwiwa".

A cikin rahotonsa, jakada Zhou ya ce, yaki da annobar, aiki ne mafi muhimmanci da gwamnatin kasar Sin take himmantuwa a kai. Kasar Sin ta sauke nauyinta yadda ya kamata, ta kuma dauki matakai masu dacewa ba tare da bata lokaci ba kuma ba tare da rufa-rufa ba, lamarin da ya samu amincewa daga kasashen duniya.

Annoba tana da hadari, amma jita-jita da tsoro sun fi hadari. Wasu kasashen da suka hada da Nijeriya suna kara karfinsu na gurfanar da wadanda suke yada jita-jita a gaban kotu.

Ranar 10 ga watan Febrairun bana, rana ce ta cika shekaru 49 da kulla huldar jakadanci a tsakanin Sin da Nijeriya. A shekarun baya, huldar da ke tsakanin kasashen 2 ta bunkasa cikin sauri, wadda ta kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri sosai. A 'yan kwanakin baya, gwamnati da al'ummar Nijeirya suna mara wa kasar Sin baya ta hanyoyi daban daban wajen yaki da annobar. Gwamnatin Sin da jama'ar kasar na gode musu sosai.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China