![]() |
|
2020-02-10 09:38:54 cri |
Tarayyar Afrika AU, ta bayyana goyon bayanta ga kasar Sin, yayin da take yaki da cutar numfashi ta Corona.
Wata sanarwa da majalisar zartarwar tarayyar ta fitar, ta ce la'akari da dangantaka mai karfi da hadin gwiwa da dadaddiyar zumuncin dake tsakanin kasashe mambobin tarayyar da kasar Sin, ministocin harkokin wajen kasashen AU, na bayyana goyon bayansu ga gwamnati da al'ummar kasar Sin, a kokarin da suke na dakile yaduwar sabuwar cutar numfashi da kwayar cutar Corona ke haifarwa da kuma yadda suke tunkarar cutar.
Sanarwar ta bayyana yakinin da kasashen ke da shi kan karfin kasar Sin na dakile yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China