Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka sun nuna yabo kan kokarin da Sin take yi wajen yaki da cutar numfashi
2020-02-05 11:34:00        cri

Kwanan baya wasu kasashen Afirka sun nuna yabo da goyon baya ga kasar Sin wajen yaki da cutar numfashi.

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya mika sako ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda ya ce, bisa goyon baya da taimakon da al'ummomin kasar Sin suka yiwa al'ummomin kasarsa, sun cimma nasarar yaki da cutar Ebola, al'ummomin kasarsa suna godiya daga zukatansu a ko da yaushe, kuma suna imanin cewa, tabbas ne al'ummomin kasar Sin za su cimma nasarar yaki da cutar numfashi. Haka zalika kuma, shugaban Guinea ya nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar, ya kuma yi fatan cewa, wadanda suka kamu da cutar za su warke cikin sauri, kuma ya ce, kasarsa tana son yin iyakacin kokari wajen ba da taimako ga kasar Sin.

Cikin sakonsa kuma, shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou ya ce, kasarsa tana goyon bayan kasar Sin, ya kuma nuna yabo matuka dangane da matakan da kasar Sin ta dauka wajen hana yaduwar cutar, yana mai cewa, tabbas ne kasar Sin za ta cimma nasarar kawar da cutar a duk fadin kasar da sauri.

Haka kuma, shugaban kasar Seychelles Danny Faure ya nuna yabo kan kokarin da kasar Sin take yi wajen yaki da cutar, da muhimmiyar rawa da masu aikin likitanci suke takawa cikin wannan aiki. Ya yabawa gwamnati da al'ummomin kasar Sin saboda babbar aniyar da suka nuna ta cimma nasarar yaki da cutar. Ya ce, yana fatan za'a iya hana yaduwar cutar da sauri, kuma kasarsa tana tare da gwmnati da al'ummomin kasar Sin.

Haka kuma, jam'iyya mai mulki ta kasar Afirka ta Kudu wato ANC ta fidda sanarwa cewa, tare da dukkanin kasashe masu son zaman lafiya, tana goyon bayan kasar Sin wajen yaki da cutar numfashi, kasar Afirka ta Kudu za ta kuma ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin tattalin arziki, ba da ilmi da ayyukan ceto da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China