Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake kasar Nijeriya ya yi bayani game da aikin yaki da cutar numfashi
2020-02-04 12:17:55        cri

A jiya ne, jakadan Sin dake tarayyar Nijeriya Zhou Pingjian, ya gudanar da taron manema labaru, inda ya yi bayani game da kokarin da kasar Sin take yi, wajen kandagarki, da yaki da cutar numfashi da kwayar cutar novel coronavirus ke haddasawa karkashin hadin gwiwar ta da sauran kasashen duniya.

Gidan telebijin na Nijeriya, da kamfanin dillancin labaru na kasar, da jaridar Leadership, da BBC, da kamfanin dillancin labaru na Reuters da sauransu sun halarci taron.

Zhou Pingjian ya sanar da yanayin da ake ciki game da kandagarki, da yaki da cutar a halin yanzu. Inda ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan tinkarar cutar, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bada umurni sau da dama game da aikin. Ya ce gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai cikin sauri, tare da yin amfani da dabarun kimiyya da fasaha, kuma a halin yanzu ana daukar matakai a duk fadin kasar, don bada jinya ga mutane masu cutar, da kare yaduwar ta.

Jakakan ya ce Sin ta jinjinawa Nijeriya bisa goyon bayanta ga gwamnatin kasar Sin, da jama'arta a fannin yaki da cutar, da daukar matakan magance cutar bisa jagorancin hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO.

Zhou Pingjian ya bayyana cewa, Sin na dora muhimmanci ga kare 'yan kasashen waje dake kasar Sin daga cutar, tare da daukar matakai masu amfani, kuma tana iyakacin kokarin ganin an biya bukatun dukkan 'yan kasashen waje, ciki har da 'yan Nijeriya dake kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China