Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka sun nuna goyon baya ga Sin wajen yaki da cutar numfashi
2020-02-04 12:19:00        cri
A kwanakin nan, wasu shugabannin kasashen Afirka, sun jinjinawa kasar Sin, a kokarinta na yakin da cutar numfashi da kwayar cutar novel coronavirus ke haddasawa, tare da nuna goyon bayansu gare ta.

Shugaban bangaren Afirka na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kuma shugaban kasar Senegal Macky Sally, ya mika wasika ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda ya nuna yabo ga kasar Sin, wajen daukar matakai masu inganci, yana mai imani da cewa, jama'ar kasar Sin za su daidaita wannan matsala.

Shugaban hukumar kungiyar AU Moussa Faki, ya bayyana a cikin wasikar da ya aikewa shugaba Xi Jinping cewa, yayin da kasar Sin ta ke kokarin tinkarar cutar numfashi, kungiyar AU na tsayawa tare da kasar Sin, tana kuma kiyaye hadin kan sassan biyu.

Haka zalika shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya bayyana cewa, kasarsa na nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka yi, wajen dakile cutar, da jajantawa iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar, tare da fatan mutanen da suka kamu da cutar za su warke cikin sauri.

A nasa bangare, shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya bayyana cewa, a madadin jama'ar kasarsa, yana mika gaishe-gaishensu, da goyon baya ga jama'ar kasar Sin, a yayin da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suke hada kansu wajen yaki da cutar.

Shi ma shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya aike da wasika ga shugaba Xi, inda ya bayyana imaninsa da goyon bayansa ga kasar Sin, wajen yaki da cutar cikin sauri.

Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso Alpha Barry, ya mika wasika ga takwaransa na kasar Sin Wang Yi, inda ya nuna goyon baya ga kasar Sin wajen yaki da cutar, da nuna yabo ga kasar Sin, bisa daukar matakai cikin sauri, da mika gaishe-gaishe ga jama'ar kasar. Ya yi imani da cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, Sin za ta dakile yaduwar cutar cikin sauri. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China