Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a yaki cutar numfashi ba tare da nuna kiyayya ga Sinawa ba
2020-02-06 11:36:10        cri

A kwanakin baya bayan nan, mashahurin dan jarida Ikkenna Emewu ya wallafa wani bayani mai taken "ya kamata a yaki cutar numfashi ba tare da nuna kiyayya ga Sinawa ba" a jaridar "The Sun" da jaridar "The Nation".

A cikin bayanin na sa, ya bayyana cewa, cutar numfashi mai tsanani ta bulla a Sin, wanda a yanzu ta tsallaka zuwa kasashe fiye da 20 na duniya. Kuma bullar cutar a kasar Sin, ya sa ana nuna wani ra'ayi na kin amincewa da Sinawa.

A kasashen Turai da Amurka, kafofin watsa labaru sun maida 'yan nahiyar Asiya a matsayin masu kawo cuta. Amma abun da ke faranta rai shi ne, kasashe da dama, da hukumomin duniya, kamar su kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, da kungiyar EU, da kasar Indiya, da kasar Pakistan, har ma kasar Vatican, suna yaba kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi, wajen yaki da cutar, tare da samar da gudummawa gare ta.

Ya ce gwamnatocin kasa da kasa, suna da alhakin jagorancin jama'a, wajen tinkarar tsoronsu kan yaki da cutar, da kawar da ra'ayin nuna damuwa da rashin sanin hakikanin yanayin da ake ciki, duba da cewa, mutane da dama suna yin iyakacin kokarin su tare da kasar Sin, wajen yaki da cutar.

Mr. Emewu ya kara da cewa, idan yana da ilmin yaki da wannan cutar, to ya so zuwa wurin da cutar ta bulla don ba da taimakon yaki da ita. Amma duk da cewa ba shi da irin wannan ilmi, yana fatan yin rubuce-rubuce don nuna goyon baya ga jama'ar kasar Sin, da jajantawa iyalai, da abokan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar. Ya ce wannan shi ne aikin jin kai da ya kamata mu yi a halin yanzu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China