Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka da dama sun jinjinawa kwazon kasar Sin a yakin da take yi da cutar coronavirus
2020-02-07 11:12:50        cri
A baya bayan nan karin kasashen Afirka da dama na ci gaba da yabawa mahukuntan kasar Sin, bisa namijin kokarin da suke yi ta hanyoyin daban daban, na dakile yaduwar cutar numfashi ta coronavirus da take addabar kasar.

Game da hakan, shugaban kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbé, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping wasikar nuna cikakken goyon bayan kasar sa, game da yakin da Sin ke yi da wannan cuta. Ya amince cewa, gwamnatin Sin ta dauki kwararan matakai, da buri na gaskiya, don haka akwai fatan Sin, tare da sauran kasashen duniya, za su yi aiki tare, ta yadda za a kai ga shawo kan wannan kalubale mai tsanani cikin kankanen lokaci.

A nasa bangare kuwa, shugaba John Pombe Magufuli na Tanzania, cikin wata wasikar ta'aziyya da jaje da ya aikewa shugaba Xi Jinping, cewa ya yi ya gamsu, da irin matakan gaggawa da gwamnatin Sin ta dauka, da kuma karfin gwiwa da karfin hali da al'ummar kasar ke nunawa, yana mai yakinin matakan da ake dauka, za su dakile yaduwar wannan annoba zuwa sauran yankunan duniya.

Shi ma shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, cikin wasikar ta'aziyya da ya aike ga shugaba Xi Jinping, bayyana yakinin kasar sa ya yi, cewa JKS da gwamnatin Sin, za su kai ga shawo kan wannan cuta yadda ya kamata.

A nasa bangare kuwa, firaministan kasar Mali Soumaïla Cissé, cikin wasikar ta'aziyya da ya aike ga firaministan Sin Li Keqiang, cewa ya yi kasar sa, na jinjinawa karfin hali, da kwarewa da gwamnatin Sin ta nuna, da ma karfin zuciya da daukacin al'ummar Sinawa ke nunawa a wannan lokaci. Ya ce al'ummar Mali na da imanin cewa, Sinawa za su ci galabar wannan annoba da ta barke. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China