Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNESCO ta baiwa Tu Youyou lambar yabo ta Equatorial Guinea mai nazari kimiyyar rayuwar Bil Adama
2020-02-11 10:52:49        cri

Jiya Litinin, UNESCO ta yi bikin baiwa masana kimiyya uku ciki hadda Tu Youyou lambar yabon kasa da kasa ta UNESCO -Equatorial Guinea kan nazari kimiyyar rayuwar Bil Adama a Addis Ababa hedkwatar tarayyar Afrika ta AU.

Bayanai na cewa, farfesa a cibiyar nazarin kimiyyar likitancin gargajiya ta kasar Sin kana wadda ta lashe lambar yabo ta Nobel a fannin likitanci a shekarar 2015, Madam Tu Youyou ta samu wannan lambar yabo da UNESCO ta bayar a wannan karo saboda gudummar da ta bayar a fannin nazarin kwayoyin cututtuta. Sai dai kuma Madam Tu Youyou ba ta halarci bikin karbar lambar yabo ba, shugaban tawagr Sin dake AU Liu Yuxi ya karbi kyautar a madadinta yayin bikin.

A hoton bidiya da Tu Youyou ta dauka dangane da wannan biki, ta nuna cewa, tana matukar farin ciki da samun wannan lambar yabo, kuma ta san babban aikin dake gabanta, tun lokacin da ta gano maganin Qinghaosu wato Artemisinin, an fara yaki da cutar malaria da maganin mai inganci. Don haka akwai bukatar kara azama wajen ganin bayan wannan cuta a duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China