Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar UNESCO ta shirya dandalin tattaunawa kan al'adun gargajiya na Sin da Afirka
2019-06-04 11:21:52        cri
An kaddamar da dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar hukumar UNESCO da Sin da Afirka, ta fuskar inganta raya al'adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni, jiya Litinin a hedkwatar UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa.

A jawabin da ya gabatar, mataimakin babban darekta mai kula da harkokin al'adu na hukumar kyautata ilimi da kimiyya da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, Ernesto Ottone Ramirez ya godewa gwamnatin kasar Sin a madadin hukumarsa, saboda goyon-bayan da take ba dandalin, inda ya yi fatan kyautata ayyukan kare al'adun gargajiyar Afirka ta hanyar yin mu'amala da karfafa hadin-gwiwar kasa da kasa.

A nata bangaren, shugabar tawagar dindindin ta kasashen Afirka dake UNESCO, kana wakiliyar tawagar Gabon dake UNESCOn, Mis Rachel Annick Ogoula Akiko ta bayyana cewa, kasashen Afirka na godewa kasar Sin saboda dimbin taimako da goyon-bayan da take ba nahiyar ta fuskokin ilimi da kimiyya da fasaha da al'adu. Tana kuma fatan tabbatar da ra'ayoyin da aka cimma tare da kasar Sin a wajen taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China