Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala taron dandalin 'yan gudun hijira na duniya na farko a Geneva
2019-12-19 10:01:19        cri

A jiya ne aka kammala taron dandalin 'yan gudun hijira na duniya na farko da aka shirya a birnin Geneva, inda aka yi alkawuran taimakawa 'yan gudun hijirar da ma al'ummomin da suka ba su mafaka.

Wata sanarwa da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta rabawa manema labarai, ta bayyana cewa, ya zuwa tsakar ranar Laraba, an cimma alkawura sama da 770 a fannoni daban-daban yayin taron, wadanda suka da samar da aikin yi, da makarantu ga yaran 'yan gudun hijira, da sabbin manufofin gwamnati, da sake tsugunar da 'yan gudun hijira, da makamashi mai tsafta. Sauran sun hada da ababen more rayuwa, da taimakawa al'ummomi da kasashen da suka baiwa 'yan gudun hijira mafaka yadda ya kamata.

UNHCR ta ce, bangaren sassa masu zaman kansu ne suka yi alkawari mafi yawa da ba a taba ganin irinsa ba, dangane de mutanen da ake tilasta musu barin muhallansu. Tana mai cewa, ba ya da alkawarun jin kai da raya kasa, kungiyoyin 'yan kasuwa sun yi alkawarin samar da taimakon sama da dala miliyan 250.

Tun da farko sai da bankin duniya ya yi alkawarin ba da sama da dala biliyan 4.7, sai bankin raya Amurka shi ma ya yi alkawarin ba da dala biliyan 1.

A jawabinsa, babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi, ya ce, yanayin 'yan gudun hijira, zai tsananta ne, idan har muka yi watsi da su, ko muka ki hada kai ko muka ki yin aiki tare, ko muka yi watsi da al'ummomin da suka ba su mafaka.

Grandi ya ce, mun ga yadda al'amura suka canja a wannan dandali na dogon lokaci.

Taron dai ya samu halartar wakilan gwamnatoci, da kungiyoyin kudi na kasa da kasa da shugabannin 'yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a fannin jin kai da raya kasa, da 'yan gudun hijira da jam'iyyun gama kai kimanin 3,000.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China