Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da UNESCO sun kulla wata yarjejeniya tallafawa ilmin sana'o'i a jami'o'in Afrika
2019-10-18 20:39:30        cri

Ran 16 ga wata agogon Paris, babbar jami'ar hukumar UNESCO Madam Audrey Azoulay da mataimakin ministan ilmi na kasar Sin Tian Xuejun suka kulla wata yarjejeniya dangane da tallafawa aikin ba da ilmin sana'o'i a manyan makarantun Afrika.

Bisa yarjejeniyar, Sin za ta zuba jarin dala miliyan 8 a cikin shekaru 4 masu zuwa don kafa wani asusun amintattu, wanda zai taimaka wajen hada kai da UNESCO don gaggauta ayyukan ba da ilmin sana'o'i a jami'o'in Afrika, ta yadda za a zakulo masu basira dake da tunanin kirkire-kirkire a Afrika, aikin da za a sa gaba shi ne kara karfin manyan makarantun Afrika, ta yadda za su samar da ilmi dake dacewa da kasuwar kwadago da samar da ilmin sana'o'i, tare kuma da kara karfin tuntuba tsakanin jami'o'i da masana'antu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China