Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar UNECA ta yi gargadi game da karuwar matsai kan mata a nahiyar Afirka saboda rashin tsaro
2020-02-04 09:31:47        cri
Shugabar hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD Vera Songwe, ta ce bai kamata kasashen Afrika su yi watsi da karuwar matsaloli da rashin tsaro da zaman lafiya ke haifarwa, wadanda ke da mummunan tasiri kan mata a fadin nahiyar ba.

Vera Songwe, ta bayyana haka ne a jiya, lokacin da take jawabi yayin wani taron manyan jami'ai kan daidaiton jinsi, wanda ya gudana jiya a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, a wani bangare na gangamin nahiyar kan inganta daidaiton jinsi.

Shugabar ta hukumar ECA, ta ce a duk lokacin da aka harba bindiga a Afrika, 'ya mace ce ke shiga mawuyacin hali tare da daina zuwa makaranta. Tana mai cewa, mata da dama na mutuwa kuma rikice-rikicen dake da alaka da cin zarafin mata na karuwa.

Ta kuma jaddada cewa kasashen Afrika dake fama da rikici yanzu haka, kamar Somalia da Sudan ta Kudu da Burundi, na da adadi mai yawa na fyade da bautar da mata ta hanyar lalata da tilasta musu karuwanci da daukar ciki da zubar da ciki da auren dole da sauransu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China