Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNESCO da StarTimes sun kulla alaka don bunkasa shirin samar da ci gaba mai dorewa na Afirka
2020-01-31 16:30:10        cri
A jiya ne ofishin shiyya na hukumar kula da ilimi, kimiya da al'adu ta MDD (UNESCO) da kamfanin StarTimes mai samar da shirye-shiryen talabijin a nahiyar Afirka, suka kulla yarjejeniya a hukumance, don taimakawa ayyukan yaki da jahilci, da daidaiton jinsi da samar da sana'o'in dogaro da kai ga matasa a nahiyar Afirka.

Da yake karin haske kan haka, darektan shiyya kana wakilin hukumar ta UNESCO Ydo Yao, ya bayyana cewa, hadin gwiwa da kamfanin na StarTimes, zai karfafa ajandar samar da ci gaba mai dorewa a Afirka ta hanyar cin gajiyar ilimi, da al'adu da fasahar kere-kere da kirkire-kirkire.

Yao ya ce, idan har aka martaba tsari da manufofi, sabuwar alakar sassan biyu za ta kara samar da damammaki da albarkatu, ta yadda za su yi tasiri, a fannonin ilimi da al'adu da jin dadin zaman jama'a, da sadarwa da bayanai.

Ya ce, hukumomin kasa da kasa, suna son yin hadin gwiwa da hukumarsa, don yayata matakan raya nahiyar ba tare da gurbata muhalli ba, a daidai gabar da nahiyar ke fama da kalubale kamar talauci, rashin daidaito da matsaloli na muhalli.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China