Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNESCO ta goyi bayan yunkurin Zambia na magance auren wuri
2019-10-25 10:07:23        cri

Daukacin kasashe mambobin hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO ne suka mara baya ga shirin Zambia na magance auren wuri da daukar juna biyu ba tare da shiri ba.

Shirin ya samu goyon baya kasancewar ya zama daya daga cikin kudurorin da aka zartar a zama karo na 207 na hukumar zartarwar UNESCO a birnin Paris na Faransa.

Zaunanniyar wakiliyar Zambia a UNESCO, Christine Kseba-Sata, ta godewa mambobin hukumar bisa goyon bayan da suka ba shirin.

Cikin wata sanarwa, wakiliyar ta bayyana damuwa kan yadda matsalolin auren wuri da daukar ciki tsakanin 'yan mata ke kara yawaita, musammam a kasashen Afrika da na kudancin Asiya, inda adadin auren wuri kan kai kaso 38 cikin 100, yayin da na daukar ciki ke kai wa tsakanin kaso 15 zuwa 25 cikin 100.

Ta ce, wannan adadi na kira ne ga kasashe mambobin hukumar su dauki mataki cikin gaggawa.

A cewarta, duk da UNESCO tana kokari sosai a kan kyautata rayuwar 'yan mata, akwai bukatar a kara zage damtse wajen rage auren wuri da daukar ciki tsakanin 'yan mata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China