Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Falasdinawa ya musanta janye kudurin adawa da yarjejeniyar zaman lafiyar Amurka
2020-02-11 10:22:52        cri
A ranar Litinin wani jami'in Falasdinawa ya musanta janye kudurin da aka gabatarwa kwamitin sulhun MDD (UNSC), wanda ke kalubalantar yarjejeniyar zaman lafiyar gabas ta tsakiya da Amurka ta tsara, mai taken "yarjejeniyar karni".

Saeb Erekat, babban sakataren kungiyar fafutukar kwato 'yancin Falastinawa ta PLO, ya fadawa manema labarai cewa rahotannin da aka yada da suke nuna janyewa kudurin ba gaskiya ba ne kuma rahoto ne marar tushe.

Kudurin nuna adawa da shirin yarjejeniyar zaman lafiyar na Amurka an gabatarwa kwamitin sulhun MDDr domin kada kuri'ar amincewa da da shi.

Erekat ya ce, tuni an riga an rarraba kudurin kuma ana aiki kansa. Da zarar an kammala komai, za'a mikawa kwamitin sulhun domin jefa kuri'a.

A yau Talata, shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas zai gabatar da jawabi a gaban kwamitin UNSC da misalin karfe 5 na yamma agogon Isra'ila.

Majdi el-Khaldi, mataimaki na musamman kan harkokin diflomasiyya ga shugaba Abbas, ya fadawa "gidan radiyon muryar Falasdinu" cewa, jawabin Mahmoud Abbas zai mayar da hankali ne kan burin Falasdinawa na samar da dauwamammen zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China