Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Abbas zai gabatar da jawabi gaban kwamitin tsaron MDD
2020-02-06 12:36:16        cri
Wakilin dindindin na Falasdinu a MDD Riyad Mansour, ya ce shugaban falasdinawa Mahmoud Abbas, zai gabatar da jawabi gaban kwamitin tsaron MDD a ranar Talatar mako mai zuwa. Mr. Mansour ya ce shugaba Abbas zai gabatar da jawabin ne game da shirin Amurka game da gabas ta tsakiya wanda shugaba Trump ya gabatar.

Mansour, ya bayyana hakan ne ta kafar radiyon falasdinu, yana mai cewa Abbas zai isa birnin New York ne a ranar Litinin, kana washe gari ya gabatar da jawabin nasa. Kaza lika zai mika daftarin dake kunshe da matsayar falasdinu ga kwamitin tsaron MDDr.

A wani ci gaban kuma, mamba a kwamitin kolin kungiyar 'yantar da falasdinawa ta PLO Saleh Ra'fat, ya shaidawa 'yan jarida cewa, daftarin da shugaba Abbas zai gabatar na kunshe da kin amincewar falasdinu da shirin Amurka game da gabas ta tsakiya. Ya ce idan Amurka ta hau kujerar na ki game da daftarin, falasdinu za ta sake gabatar da shi gaban babban zauren MDD.

Jami'in ya ce suna sa ran kudurin na su, zai samu gagarumar amincewa a babban zauren MDD, kuma suna fatan za a yi Allah wadai da matakan rashin adalci da Isra'ila ke aiwatarwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China