Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin MDD ya bukaci a kawo karshen mamayar da Yahudawa ke yiwa yankunan Palastinawa
2019-10-29 10:55:00        cri
Wakilin musamman na MDD a aikin wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya Nickolay Mladenov, ya bayyana a ranar Litinin cewa, cigaba da mamayar da Isra'ila ke yiwa yankunan Palastinawa shine babbar barazanar zaman lafiyar yankin, don haka ya bukaci su dena mamayar.

Da yake jawabi ga kwamitin sulhun MDD ta hanyar shirin bidiyo na kai tsaye daga birnin Jerusalem, Mladenov ya bayyana cewa, akwai wasu rahotannin dake bayyana cewa hukumomin Isra'ila sun tsara wani shirin kara gina wasu rukunin gidaje a yammacin kogin Jordan a watan da ya gabata, sai dai ba'a bayyana hakikanin yawan gidajen ba.

Yace ko da babu wannan shiri na baya bayan nan, adadin yawan matsugunan da aka amince za'a gina a yankunan cikin 2019 sun zarce na shekarar 2018.

A cewarsa, mamayar da yahudawan ke yi sun saba dokokin kasa da kasa, kuma shi ne babbar barazanar zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya.

Babban wakilin MDDr a gabas ta tsakiya yace, ana cigaba da rusawa da kuma kwace matsugunai mallakin al'ummar Palastinawa a fadin yankunan yammacin kogin Jordan, a watannin baya bayan nan ma kimanin gidaje 51 aka rusa kana Palastinawa 80 aka tilastawa ficewa daga mahallansu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China