Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Duk wata yarjejeniyar zaman lafiya za ta kare idan Netanyahu ya mamaye zirin Jordan
2019-09-11 10:24:35        cri

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya yi gargadi a jiya cewa, duk wata yarjejeniyar zaman lafiya za ta kare idan Firaministan Isra'ila ya yi yunkurin mamaye zirin Jordan, dake yankin yammacin kogin Jordan.

Mahmoud Abbas, ya ce za a datse yarjeniyoyin da aka cimma da Isra'ila, idan ta ayyana ikonta a kan mataccen teku ko Zirin Jordan ko wani bangare na yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye a 1967.

Shugaban na Falasdinu, ya ce suna da hakkin kare 'yancinsu da cimma burinsu bisa dukkan hanyoyin dake akwai, ba tare da la'akari da sakamakon da hakan zai haifar ba, tun da matakin Netanyahu, ya saba da halalci da kuma dokokin kasa da kasa.

Jawabin na Mahmoud Abbas, na zuwa ne bayan Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya sanar da cewa, Zirin Jordan zai koma karkashin Isra'ila idan aka sake zabarsa a zaben da za a yi ranar 17 ga wata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China