Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Netanyahu na duba yiwuwar soke manyan zabuka da aka shirya yi a Isra'ila cikin watan Satumba
2019-06-26 12:01:46        cri
Jam'iyyar Likud dake karkashin Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu, ta ce Firaministan na duba yiwuwar soke manyan zabukan majalisar dokokin kasar (Knesset) da aka shirya yi ranar 17 ga watan Satumba.

An gudanar da zabukan baya-bayan nan a kasar ne a ranar 9 ga watan Afrilu, sai dai Netanyahu ya gaza kulla kawance da akalla mambobin majalisar 61 daga cikin 120, bayan jami'iyyar Likud ta masu ra'ayin mazan jiya ta lashe kujeru 35.

Jam'iyyu masu ra'ayin mazan jiya sun samu jimilar kujeru 65 a zabukan, sai dai tsohon ministan tsaron kasar Avigdor Lieberman,kuma shugaban jam'iyyar Yisrael Beiteinu, ya ki shiga kawancen, wanda ya kai ga kada kuri'ar soke majalisar domin gudanar da sabbin zabuka.

Sai dai saboda tsadar gudanar da karin zabuka, da aka yi kiyasin za su lakume kudin kasar New Shekels biliyan 2, kwatankwacin dala miliyan 557, da kuma bukatun da galibin mambobin majalisar suka gabatar, shugabanta Yuli Edelstein ya gabatar da soke karin zabuka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China