Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin Sulhu na MDD zai gudunar da taro dangane da shirin zaman lafiya na yankin gabas ta tsakiya da Amurka ta gabatar
2020-02-03 12:36:28        cri
Kwamitin sulhu na MDD zai gudanar da taro a cikin mako mai zuwa, domin tattauna shirin zaman lafiya na yankin Gabas ta Tsakiya mai sarkakiya, wanda Amurka ta gabatar.

Wata majiya ta bayyana cewa, Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas da Jakadan Isra'ila a MDD, Danny Danon, za su halarci taron, tana mai cewa Jakadun Falasdinu na shirya kudurin da zai rushe shirin zaman lafiyar mai tsarkakiya, duk da cewa akwai yuwuwar Amurka ta hau kujerar na ki kan kudurin.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Isra'ila a MDD ya fitar ta ruwaito cewa, yanzu haka, Danny Danon, na tattaunawa da takwarorinsa dake kwamitin domin neman goyon bayansu kan shirin zaman lafiyar wanda na hadin gwiwa ne tsakanin Amurka da Isra'ila, tare kuma da kin goyon bayan duk wani yunkurin Falasdinu na adawa da shi.

A ranar 28 ga watan Junairu ne, Shugaban Amurka Donald Trump, ya gabatar da shirin zaman lafiya na yankin gabas ta tsakiya, wanda kuma ake kira da "shirin zaman lafiya na karni", dake neman kafa kasashe 2, tare kuma da ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila da ba a iya raba shi ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China