Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hanyar siyasa ce kadai za ta warware matsalar Falesdinu, in ji wakilin Sin
2020-01-22 10:37:20        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya bayyana a jiya Talata cewa, ta hanyar siyasa ne kadai za a iya warware matsalar Falesdinu, kuma daukar matakan soja ba zai taimaka ko kadan wajen warware matsalar ba.

Yayin taron tattaunawa kan yanayin yankin Gabas ta Tsakiya da batun Falesdinu, wanda kwamitin sulhu na MDD ya kira a wannan rana, Zhang Jun ya ce, kasar Sin tana sa kaimi ga bangarorin da abun ya shafa, da su yi hadin gwiwa, da dakatar da dukkanin matakan soja, da kuma daina gabatar da labarai masu hura wutar tashin hankali.

Kaza lika Sin na fatan sassan za su kaucewa daukar matakan da za su bata mutuncin wani ko wata, domin magance tabarbarewar yanayin yankin, da kuma kiyaye yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, ta yadda za a samar da dama mai kyau ga bangarorin da abin ya shafa wajen komawa teburin shawarwari.

Haka kuma, Zhang Jun ya jaddada cewa, "daftarin kasashe guda biyu" shi ne hanya kadai da ta dace a bi, wajen warware sabanin dake tsakanin Isra'ila da Falesdinu, kuma kafa kasar Falesdinu mai 'yancin kai, ikon 'yan Falesdinu ne da ba wanda zai iya kwacewa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China