Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare janar na MDD ya bayyana cikakken goyon bayansa ga kasar Sin a kokarinta na kawar da annobar da ta barke
2020-01-28 16:28:35        cri
A ranar 27 ga watan Janairu, Ambasada Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya gana da babban sakataren MDD Antonio Guterres, domin gabatar masa da halin da ake ciki da irin namijin kokarin da kasar Sin ke yi wajen kandagarki da kuma magance annobar cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haifarwa da ta barke a kasar.

Zhang Jun ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin tana bada muhimmanci matuka wajen tinkarar annobar da kuma dakile ta, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dauki kwararan matakai da kuma bayar da muhimmin umarni domin dakile annobar.

A halin da ake ciki, matakan da ake dauka wajen tinkarar annobar sun kai matsayin koli, kuma kasar Sin tana da kwarin gwiwar samun nasarar yin kandagarki da kuma shawo kan cutar.

Guterres ya ce, a wannan matsanancin hali da ake ciki, MDD tana cikakken goyon bayan kasar Sin da al'ummar Sinawa. MDDr ta yabawa kokarin da kasar Sin ke yi, kuma tana da yakinin matakan da kasar Sin ke dauka wajen tinkara da kuma shawo kan annobar cutar coronavirus zasu yi tasiri, kuma a shirye take a koda yaushe ta bayar da dukkan goyon baya da tallafi ga kasar Sin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China