Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ce ya kamata kwamitin sulhu na MDD ta dage takunkuman da ta kakabawa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
2020-02-01 16:45:40        cri
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce ya kamata kwamitin sulhu na majalisar, ya dage takunkuman da ya sanyawa jamhuriyar Afrika ta Tsakiya nan bada dadewa ba.

Da yake jawabi yayin taron kwamitin a jiya, Wu Haitao, ya ce baki dayan yanayin siyasa da tsaron Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na tafiya kan tafarkin da ya dace.

Ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta jajirce wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma, kuma ta cimma nasarori wajen aiwatar da ka'idojin dage takunkuman sayar mata da makamai.

Ya ce har kullum, kasar tana ammana cewa, takunkuman hanya ce ta taimakawa kasar dawo da zaman lafiya da harkokin jama'a yadda ya kamata nan bada jimawa ba.

Don haka, ya yi kira ga kwamitin ya dage takunkuman bisa la'akari da ainihin halin da kasar ke ciki, musamman burin gwamnatin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China