2020-02-02 19:43:52 cri |
A sanarwar da kakakinsa ya fitar, babban sakataren MDD ya nuna damuwa matuka game da ayyukan da sojoji ke gudanarwa a shiyyar.
Babban sakataren ya ce hare-haren da ake kaiwa kan fararen hula da kuma kan wasu muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, kamar asibitoci, ba abin da za'a lamunta ba ne.
Sanarwar ta ce, duk wani nau'in aikin sojoji daga kowane bangare, wanda ya hada da daukar matakai kan kungiyoyin ta'addanci da wanda kungiyoyin ke kaddamarwa, dole ne su mutunta muhimman dokokin jin kan bil adama na kasa da kasa, wanda ya kunshi baiwa fararen hula cikakkiyar kariya.
Guterres ya nanata cewa babu wani matakin soji da zai iya warware matsalolin tashin hankali. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China