Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin Sulhu na MDD ya sabunta takunkumansa kan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
2020-02-01 16:50:03        cri
Kwamitin sulhu na MDD, ya amince da kudurin tsawaita takunkumansa kan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da watanni 6.

Bisa la'akari da yadda yanayin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ke ci gaba da zama barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa a yankin, kudurin mai lamba 2507, ya yanke shawarar sabunta takunkuman kwamitin, ciki har da na haramta sayar da makamai ga kasar, har zuwa ranar 31 ga watan Yulin bana.

Har ila yau, ya kuma tsawaita wa'adin aikin ayarin kwararru, wanda zai taimakawa kwamitin wajen aiwatar da takunkuman, har zuwa wancan lokaci.

Wannan ne karon farko da aka sabunta takunkuman kasar, tun bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin kasar da kungiyoyi 14 masu dauke da makamai, a birnin Bangui a ranar 6 ga watan Fabrerun 2019. Kuma tun daga wancan lokaci, an samu raguwar fito na fito tsakanin kungiyoyin da dakarun tsaron kasar da kuma rikice-rikicen dake da alaka da keta hakkokin bil adama, idan aka kwatanta da shekarar 2018.

Tun cikin shekarar 2012, Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta tsunduna yakin basasa, wanda ke da alaka da kabilanci da kuma addini. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China