Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Tubulin ci gaban tattalin arzikin Sin mai dogon zango bai sauya ba
2020-02-11 09:33:23        cri

Shugaban kasar Sin, kuma sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS, Xi Jinping, ya ce tubulin tattalin arzikin kasar mai dogon zango bai sauya ba, kuma tasirin cutar numfashi ta Corona kan tattalin arzikin na gajeren lokaci ne.

Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin aikin sojin kasar, ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake rangadin ayyukan aiwatar da matakan kariya daga cutar corona da kuma yadda ake kokarin dakile yaduwarta a birnin Beijing.

Ya bukaci a kara zage damtse wajen rage tasirin cutar kan tattalin arziki, da kuma cimma burikar samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a bana.

Har ila yau, ya yi kira da a kara mayar da hankali kan aikin don kaucewa kora ko dakatarwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China