Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu karuwar kayayyakin da masana'antu ke samarwa a shekarar 2019 a Beijing
2020-02-02 15:35:34        cri
Hukumar kididdiga ta majalisar gudanar da mulkin birnin Beijing ta bada rahoton cewa an samu bunkasar adadin kayayyakin da masana'antu ke samarwa a Beijing a shekarar 2019.

Darajar kayayyakin da manyan kamfanonin suka samar ya karu da kashi 3.1 idan an kwatanta da farashin kayayyakin da aka samar a makamancin na shekarar 2018.

Daga cikin jimillar kayayyakin, an samu karuwar yawan na'urorin kwamfuta, kayayyakin sadarwa da sauran kayayyakin latironi da aka samu karuwar kashi 9.9 bisa 100, sannan bangaren na'urorin dumama dakuna ya karu da kashi 8.2 bisa 100, yayin da bangaren hada magunguna ya karu da kashi 6.2 bisa 100, a cewar hukumar kididdigar.

Bangaren kamfanonin hada motoci kuwa, ya samu tagomashi da karin kashi 2.7 bisa 100, duk da rashin cinikin da bangaren ya fuskanta.

Baki daya kudaden shigar da manyan masana'antun suka samu ya zarce yuan triliyan 1.94, kwatankwacin dala biliyan 282.9, inda aka samu karin kashi 3 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarar 2018. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China