Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: Kasashen Afirka da ba su da albarkatun kasa za su fi samun bunkasuwa a shekarar 2020
2019-12-20 09:23:59        cri

Tsohon mashawarcin kungiyar tarayyar Afirka da hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka(UNECA) kan harkokin tattalin arziki, Contantinos Bt. Constantinos, ya bayyana cewa, idan har kasashen Afirka da ba su da albarkatun kasa, suka samu girbin amfanin gona mai yawa da bukatun masu sayayya da karuwar zuba jari, akwai yiwuwar za su fi samun bunkasuwar tattalin arziki a shekarar 2020.

Ya ce, bayanai na nuna cewa, a shekarar 2019, kasashe marasa albarkatun kasa, irin su, Senegal, da Rwanda da Cote d'Ivoire, sun samu ci gaban cikin sauri. Sai dai kuma, masanin ya ce, kasashe dake kan gaba wajen fitar da kayayyaki zuwa ketare, kamar Aljeriya da Najeriya da Afirka ta kudu, wadanda ake ganin tattalin arzikinsu na dan da ja-baya, na iya sanya matsakaicin ci gaban tattalin arzikin Afirka ya yi baya a shekarar 2020.

Contantinos ya ba da shawarar a rika fitar da kayayyakin da aka sarrafa da kaddarori zuwa kasashen Afirka, maimakon kayayyakin da ba su da inganci, a wani mataki na hanzarta ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci da ma yadda tsarin tattalin arzikin nahiyar zai kaucewa fuskantar kalubale.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China