Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taron raya tattalin arziki a Beijing
2019-12-12 20:15:21        cri
An yi taron aikin raya tattalin arziki na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a nan birnin Beijing tsakanin ranar 10 zuwa 12 ga wata, babban sakataren JKS, shugaban kasar kuma shugaban kwamitin aikin soja na kasar Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi yayin taron, inda ya gabatar da aikin raya tattalin arzikin kasar na shekarar 2019, da ma yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki yanzu, sannan ya fito da shirin aikin a shekarar 2020 dake tafe.

Yayin taron, an yi nuni da cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana gudana yadda ya kamata, kana kasar Sin ta samu babban sakamako a fuskar yaki da talauci da magance rikicin hada-hadar kudi da kuma kyautata muhallin halittu masu rai da marasa rai, ana iya cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba yayin da take kokarin gina al'umma mai matsakaicin wadata.

Kana an tabbatar da cewa, kasar Sin za ta kammala aikin yaki da talauci daga dukkan fannoni nan da karshen shekarar 2020, musamman ma a yankuna mafiya fama da talauci dake Tibet da Xinjiang da lardunan Sichuan da Yunnan da Gansu da Ningxia, tare kuma da kokarin hana masu fama da talauci sake shiga mawuyancin hali.

Babban taron raya tattalin arziki da aka shirya a Beijing, fadar mulkin kasar Sin ya nuna cewa, a shekarar 2020 ya kamata kasar Sin ta mayar da hankali kan kirkire-kirkire da gyare-gyare da bude kofa, matakin da zai taimaka wajen karfafa yin takara a fannin tattalin arziki da bunkasa gina tsarin tattalin arziki na zamani.

Bugu da kari, taron ya yi imanin cewa, a shekarar 2020 kasar Sin za ta ci gaba da fadada matakanta na bude kofa ga ketare. Kasar Sin za ta karfafawa baki masu sha'awar zuba jari a cikin kasar gwiwa da ma ba su kariya bisa doka, da ci gaba da rage fannonin da aka haramtawa baki zuba jari a baya, da bunkasa cinikayyar ketare, da daidaita da kara fadada amfani da jarin waje, da rage haraji da kudaden da ake biya, da kara gina tashar ruwa maras shinge a Hainan. Sauran fannonin sun hada da inganta manufofin zuba jari da ayyukan hidima kan shawarar ziri daya da hanya daya, da hanzarta cimma matsaya kan yarjeniyoyin cikakayya da Sin ta cimma da sauran kasashe(Jamila, Yaya Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China