Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NBC: Tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da kaso 6.1 cikin dari a shekarar 2019
2020-01-17 12:11:45        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin, ta sanar a yau Jumma'a cewa, tattalin arzikin kasar ya bunkasa da kaso 6.1 cikin 100 a shekarar 2019, kan shekarar da ta gabata, wannan adadi ya yi daidai da abin da gwamnati ta yi hasashen cimmawa na kaso 6 zuwa kaso 6.5 cikin 100, kuma shi ne mafi yawa a fannin saurin bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya, matakin da ya sa Sin take sahun gaba a wannan fanni, har ta kai matsayin farko a kasashen da suka mallaki kudi fiye da dala triliyan 1.

Alkaluma na nuna cewa, karuwar tattalin arzikin Amurka a shekarar 2019 ya kai kaso 2.3 cikin dari, yayin da saurin bunkasuwar Japan da kasashen dake amfani da kudin Euro, ya kai sama da kaso 1 cikin dari, adadin na Indiya kuma ya kai kaso 5 cikin dari.

A shekarar 2019 da ta gabata, GDPn kasar ta Sin ya kai RMB Yuan triliyan 99 da biliyan 86 da miliyan 500.

Ya zuwa karshen shekarar 2019, yawan al'ummar babban yankin kasar Sin ya zarce biliyan 1.4, adadin da ya karu da mutane miliyan 4.67 kan na karshen shekarar da ta gabace ta.

Alkuluma na nuna cewa, a shekarar 2019, adadin kudin shigar kowane Basine ya kai Yuan 30,733, kwatankwacin dala 4,461.95, wanda ya karu da kaso 5.8 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata.

Har ila, a shekarar 2019, kayayyakin bukatun yau da kullum da aka sayar, wanda shi ne babban ma'aunin dake nuna bunkasuwar ci maka, ya karu da kaso 8 cikin 100. A dai shekarar da ta gabata, darajar kayayyakin bukatun jama'a da aka sayar, ta kai RMB Yuan triliyan 41.16. kimanin dala Triliyan 5.99. Cinikayya ta Intanet tana ci gaba da bunkasa, inda a shekarar ta 2019, sashen ya yi cinikayar da darajar ta kai Yuan Triliyan 10, adadin da ya karu da kaso 16.5a. (Ibrahim Yaya&Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China