Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yaba rawar da kasar Sin ta taka a ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD
2019-06-28 09:49:02        cri
Mashawarcin soja na MDD kan ayyukan wanzar da zaman lafiya Carlos Humberto Loitey, ya yaba da irin rawar da kasar Sin ta taka a ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Jami'in na MDD wanda ya bayyana hakan a gyefen taron dandalin masana ayyukan wanzar da zaman lafiya na kungiyar ASEAN karo na 7 dake gudana a birnin Qiandao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin, ya bayyana cewa, dakarun kota-kwana na kasar Sin dake aikin wanzar da zaman lafiya, sun taimakawa tawagogin MDD dake aikin kiyaye zaman lafiya matuka.

Ya ce, ya zuwa watan Fabrairun shekarar 2019, dakarun kasar Sin 8,000 dake aiki karkashin dakarun kiyaye zaman lafiya na kota-kwana na MDD, sun kammala shirin samun horo. Kuma sassa biyar daga cikinsu sun kai mataki na uku cikin matakai hudu na shirin kota-kwana.

Loitey ya ce, kasar Sin na daga cikin kasashen dake ba da gagarumar gudummawa ga masu kayan sarki dake aikin kiyaye zaman lafiya, ta kuma tura dakarunta zuwa kasashe kamar Sudan da Sudan ta kudu da Lebanon da Jamhuriyar demokiradiyar Congo da Mali domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China