Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in MDD ya aika sakon taya murnar sabuwar shekarar Sinawa bisa kalandar gargajiya
2020-01-23 10:14:16        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, a ranar Laraba ya aika sakonsa na taya murnar sabuwar shekarar Sinawa bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, inda ya godewa kasar Sin da al'ummar Sinawa bisa goyon bayan da suke baiwa MDD.

A sakon da ya aika ta bidiyo, Guterres, ya fada da yaren Sinanci "Chun Jie Kuai Le" wato "Barka da sabuwar shekara" a matsayin kalmar farko cikin sakon gaisuwar da ya aikawa al'ummar Sinawa.

Ya jaddada cewa, shekarar 2020 ake cika shekaru 75 da kafuwar MDD, kuma shekaru goman farko na cikar wa'adin shirin muradun samar da dawwamammen ci gaba na MDD.

Ya ce "a wannan yanayi da ake fuskantar tashe-tashen hankula da rarrabuwar kai, tilas ne mu yi aiki tare domin nemawa duniya mafita game da manyan kalubaloli, kuma mu gina makoma mai kyau ga dukkan bil adama," in ji mista Guterres.

Ya godewa kasar Sin da al'ummar Sinawa saboda goyon bayan da suke baiwa MDD, da ra'ayin bangarori daban daban, kana ya yiwa al'ummar Sin fatan alheri da samun koshin lafiya, da farin ciki, gami da nasarori.

Sabuwar shekarar Sinawa bisa kalandar gargajiya, ko kuma "shekarar bera", ta zo daidai da ranar 25 ga watan Janairun wannan shekara, kuma shi ne biki mafi muhimmanci ga Sinawa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China