Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta tabbatar da kai hari kan ginin cibiyar aikin jin kai a arewa maso gabashin Najeriya
2020-01-21 11:16:47        cri
Jami'in MDD ya bayyana a ranar Litinin cewa, wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun afkawa cibiyar bayar da tallafin jin kan al'umma ta MDD dake garin Ngala a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, inda suka lalata daya daga cikin ginin cibiyar.

A wata sanarwar da Edward Kallon, jami'in kula da shirin jin kai na MDD dake Najeriya ya fitar an ce, ginin shi ne wajen da jami'an aikin jin kan na MDDr ke zama cikinsa, kana shi ne babban muhallin jami'an a garin Ngala, an kaiwa ginin hari ne a ranar Asabar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China