Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF na da yakinin tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da kasancewa mai juriya
2020-02-04 10:21:23        cri

Shugabar asusun bada lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva, ta ce asusun na mara baya ga kasar Sin a kokarin da take na yaki da barkewar kwayar cutar Corona, kuma yana da yakinin tattalin arzikin kasar na da juriya.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter da kuma irinsa da ta wallafa a dandalin sada zumunta na kasar Sin wato Weibo, Kristalina Geogieva ta jajantawa dukkan wadanda barkewar cutar numfashi ta Corona ta shafa.

Ta kara da cewa, suna goyon bayan kokarin da kasar Sin ke yi na tunkarar cutar, ciki har da wasu manufofin kudi da ta dauka a baya bayan nan. Tana mai cewa suna da yakinin tattalin arzikin kasar zai ci gaba da kasancewa mai juriya.

Har ila yau, yayin wani taron manema labarai a baya-bayan nan, kakakin asusun Gerry Rice, ya nuna goyon baya ga yakin da kasar Sin ke yi da barkewar cutar, inda ya ce, a bayyane yake cewa hukumomin kasar sun dauki batun da muhimanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China