Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF ya daga matsayin hasashen karuwar tattalin arzikin Sin na shekarar 2020
2020-01-21 12:18:08        cri

Jiya Litinin, Asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya fidda sabon rahoton "hasashen tattalin arzikin duniya", inda ya daga matsayin hasashen da yayi kan karuwar tattalin arzikin Sin a watan Oktoban bara daga kashi 5.8% zuwa kashi 6%.

Cikin rahoton, ya yi hasashen cewa, a shekarar 2020 saurin karuwar tattalin arzikin Sin zai kai kashi 6%, a shekarar 2021 kuma, adadin zai kai kashi 5.8%. babbar masaniyar tattalin arzikin ta IMF Gita Gopinath ta ce, dalilin da ya sa aka rage saurin karuwar tattalin arzikin Sin shine kwaskwarimar da ta yi kan tsarin tattalin arziki.

Ko da asusun ya daga hasashen karuwar tattalin arzikin Sin, amma ya rage hasashen da yayi kan karuwar tattalin arzikin duniya. Kuma bisa hasashen da ya yi, an ce, a shekarar 2019, saurin karuwar tattalin arzikin duniya ya kai kashi 2.9%, a bana, adadin zai kai kashi 3.3%, sa'an nan, adadin zai kai kashi 3.4% a shekarar 2021. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China