Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karfin kudin Sin a matsayin kudin da aka adana ya kara inganta
2020-01-08 11:05:55        cri

Kididdigar asusun ba da lamuni na duniya IMF ta ce, ya zuwa karshen watan Satumban bara, yawan kudin Sin RMB da manyan bankunan kasashen duniya ke adanawa ya kai kashi 1.97 zuwa 2.01 cikin dari, adadin da ya kai sabon matsayi tun daga watan Octoban shekarar 2016, lokacin da asusun IMF ya gabatar da irin wannan rahoto. Mai magana da yawun hukumar kula da musayar kudade ta kasar Sin, madam Wang Chunying ta ce, lamarin ya bayyana cewa, karfin kudin Sin a matsayin kudin da ake adanawa ya kara inganta.

Ban da wannan kuma, kididdigar ta nuna cewa, manyan bankunan kasashe daban-daban na kokarin adana kudaden ketare daban-daban a shekarun baya-baya nan. Alkaluman da asusun IMF ya fitar, sun nuna cewa, yawan kudaden da aka adana na dala ya ragu zuwa kashi 61.78 cikin dari a karshen watan Satumban bara daga kashi 65.17 cikin dari na karshen watan Disamban shekarar 2014, duk da haka kudin dala na kan matsayin farko a fannin kudaden da ake adanawa a fadin duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China