Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin IMF: Illar da cutar numfashi ke yi wa tattalin arziki ba zai shafi lokaci mai tsawo ba
2020-02-01 15:52:30        cri

Kakakin Asusun ba da lamuni na duniya IMF, Gerry Rice ya ce babu shakka cutar numfashi da kwayar cutar Corona ke haifarwa, wadda ta barka a lokacin bikin sabuwar shekarar gargarjiya ta kasar Sin, ya yi tasiri ga zirga-zirga da sayayya, har ma ya haddasa rashin tabbas ga tattalin arzikin kasar. Amma, irin illar da cutar ke yi wa tattalin arzikin Sin ba zai shafi lokaci mai tsawo ba. Yana mai cewa, bayan shawo kan annobar, da komawar harkokin kasuwanci yadda ya kamata, tattalin arzikin Sin zai farfado.

Ban da wannan kuma, Gerry Rice ya ce, Sin kasa ce mai girma a fannin tattalin arziki, don haka tana da albarkatu da ma aniyar tinkarar matsalar da cutar ka iya haifarwa.

Har ila yau, ya jinjinawa yadda gwamnatin Sin ke tinkarar annobar, inda ya ce yadda ta hada kai sosai da hukumar lafiya ta duniya WHO da ma sauran bangarorin da abin ya shafa wajen bayar da bayanai kan cutar, ya yi amfani sosai wajen tunkarar cutar. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China