Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF ya jaddada cewa darajar kudin musaya na Sin na bisa turba
2019-08-10 16:39:34        cri

Wani sabon rahoton asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya ce an yi kiyasin darajar kudin musaya na Sin a shekarar 2018, ya yi daidai da tanadin manufofi da ka'idoji.

A cewar rahoton, asusun rara na kasar Sin ya sauka da kusan maki daya zuwa kaso 0.4 na alkaluman GDP a shekarar 2018, kuma an yi hasashen zai kasance kan kaso 0.5 na GDP a bana.

Jeffrey Sachs, babban mashawarcin MDD, kuma fitaccen shehun malami a fannin nazarin harkokin tattalin arziki a Jami'ar Columbia, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, rahoton na IMF, ya nuna karara cewa, kasar Sin ba ta rage dajarar kudinta ba, kuma mizanin hada-hadarta a ketare na bisa ka'ida.

Shehun malamin ya ce, ikirarin baitumalin Amurka cewa, Sin na rage darajar kudinta da gangan, ba shi da tushe, kuma batu ne na siyasa da ya dogara kan abun da shugaba Trump ya wallafa a shafin Tweeter, mai maimakon sahihan bayanai.

Cikin sabon rahoton wanda aka fitar a jiya, daraktocin zartarwa na asusun IMF, sun kuma jinjinawa hukumomin kasar Sin, bisa ci gaban da aka samu na aiwatar da gyare-gyare, musammam wajen rage kalubalen da bangaren kudi ka iya fuskanta da kara bude kofa, inda kuma suka jaddada muhimmancin aiwatar da gyare-gyare kan harkokin kudi, wanda zai iya inganta samar da ci gaba cikin gajere da matsakaicin zango.

Da suke maraba da kudurin kasar Sin kan inganta huldar kasa da kasa da gudanar cinikayya bisa tanadin doka, daraktocin sun amince cewa, ya kamata a gaggauta warware takaddamar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ta hanyar ingantacciyar yarjejeniya da za ta kaucewa raina tsarin kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China