Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana: Harajin da Amurka ta sanyawa Sin ba zai warware gibin cinikayya tsakanin kasashen biyu ba
2019-08-22 20:22:47        cri
Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi gargadin cewa, 'yan kasuwar kasar Amurka da masu sayayya na dora laifi kan harajin da gwamnatin Amurka ta sanyawa kayayyakin kasar Sin, kuma matakin ba zai magance gibin cinikayya tsakanin manyan kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya ba.

A wani sakon da suka walkafa, mai taken "tsananta takaddamar cinikayya" Gustavo Adler, Luis Cubeddu da Gita Gopinath, sun bayyana cewa, sanya karin haraji, mayar da martani ne wajen magance kara daga darajar kudi saboda "kara haraji da musayar darajar kudi kowanne aikinsa daban."

Gustavo Adler,shi ne mataimakin shugaban sahen kula da harkokin bincike a asusun IMF, Luis Cubeddu, shugaban sashen tattalin arziki, sai Gita Gopinath, babbar masaniyar harkokin tattalin arziki.

Masana binciken na IMF, sun bayyana cewa, matsakaicin harajin da Amurka ta sanyawa kayayyakin Sin da ake shigarwa cikin kasar, ya karu da kimanin kaso 10 cikin 100 tun a farkon shekarar 2018, kuma zai iya karuwa da misalin kaso 5 cikin 100, idan har shirin karin harajin da Amurkar ta sanar ya fara aiki.

Sharhin na cewa, 'yan kasuwar Amurka da masu sayayya dai su ne suke dandana kudarsu. Saboda idan har darajar kudin kasar ya yi wani tasiri, shi ne zai nuna farashin dala da 'yan kasuwan kasar Sin za su yi amfani da shi, saboda yadda ake cinikayya da dalar

Don haka, kara sanyawa juna haraji, ba zai magance gibin cinikayya dake tsakanin kasasahen biyu, kamar yadda suke tunani ba. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China