Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tasirin da annobar cutar numfashi ta yi wa tattalin arzikin Sin zai zama na gajeren lokaci
2020-02-03 13:35:08        cri

Yau Litinin, mataimakin shugaban kwamitin neman bunkasuwa da yin kwaskwarima na kasar Sin Lian Weiliang, ya bayyana a birnin Beijing cewa, tasirin da annobar cutar numfashi ya yi wa tattalin arzikin kasar, zai danganta kan yadda ake aiwatar da matakan hana yaduwar cutar, da kuma sakamakon da za a samu nan gaba. Kuma tasirin zai zama na gajeran lokaci ne, wanda ba zai canja kyakyyawan yanayi na raya tattalin arzikin kasar ba.

Yayin taron manema labarai da aka yi a yau Litinin, Lian Weiliang ya ce, wasu sun yi hasashe bisa irin tasirin da barkewar cutar SARS ya yiwa tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2003, amma, halin da kasar Sin ke ciki ba kamar na shekarar 2003 ba, yanzu, kasar Sin ta sami karin karfi a fannonin tattalin arziki, da samar da kayayyaki, da kuma fuskantar da harkokin gaggawa. Ya ce Sin tana da imani wajen cimma nasarar dakatar da yaduwar cutar a duk fadin kasar, da kuma rage tasirin da hakan zai yi ga tattalin arzikin kasar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China