Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya kira taro kan gudanar da ayyukan maganin cutar numfashi bayan hutun bikin bazara
2020-02-01 15:46:38        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya shugabanci taron tawagar kwamitin yakar cutar numfashi a jiya Juma'a, inda ya nuna cewa, la'akari da kammalar hutun bikin bazara nan ba da jimawa ba, abu mafi muhimmanci yanzu shi ne gudanar da aikin rigakafi da maganin cutar da kila masu komawa aiki za su iya haddasawa. Yana mai cewa, ya kamata wurare da ma hukumomi daban daban, su gudanar da wannan aiki cikin tsanake domin hana yaduwar cutar.

Li Keqiang, wanda kuma zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ne, kuma shugaban tawagar kwamitin yakar cutar numfashin, ya kara da cewa, matakan da za a dauka sun hada da: da farko dai, a tsara shirin komawa aiki ba cikin sa'i daya ba, wato a yarda da tsawaita lokacin hutun a lardin Hubei. Sannan, a tsawaita lokacin hutun ga wadanda ke lardin Hubei yanzu haka, amma wajen aikinsu na wasu wurare daban daban, a wani bangare na kokarin maganin cutar. Na biyu kuma, a gudanar da aikin zirga-zirga yadda ya kamata, da ma mai da hankali kan aikin zirga-zirgar mutanen da batun ya shafa. Na uku kuwa shi ne bada muhimmnci kan rigakafin cutar a kan hanyoyin sufuri. Na hudu kuma, a mayar da hankali kan zirga-zirgar mazauna wuraren da cutar ta fi kamari. Na karshe kuwa shi ne, tabbatar da jigbe isassun ma'aikata wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka, kamar wadanda suka shafi zirga-zirga da maganin cutar da dai sauransu. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China