Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus 2,590 da wadanda da suka mutu 45
2020-02-02 15:42:15        cri
Hukumomin lafiyar kasar Sin sun sanar a yau Lahadi cewa an samu rahoton adadin sabbin mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta coronavirus kimanin 2,590, yayin da sabbin mutanen da suka mutu ya kai 45 a ranar Asabar daga larduna 31 gami da bangaren ayyuka da gine-gine na yankin Xinjiang.

Dukkan mutanen da suka mutu daga lardin Hubei ne, kamar yadda hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar.

Hukumar ta ce, an bayyana wasu sabbin mutanen kimanin 4,562 da ake zaton sun kamu da cutar.

Sannan a ranar Asabar, wasu mutane 315 sun shiga cikin matsanancin hali sakamakon cutar, yayin da aka sallami wasu mutane 85 daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

Baki daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin kasar Sin ya kai 14,380 ya zuwa karshen ranar Asabar, in ji hukumar, sannan jimillar mutane 304 ne suka mutu a sanadiyyar cutar a duk fadin kasar Sin.

Hukumar lafiyar ta kara da cewa, mutanen da suka kamu da cutar 2,110 ne suke cikin matsanancin hali, sai kuma mutane 19,544 da ake zaton sun kamu da kwayar cutar.

Adadin mutanen da aka sallama daga asibitoci ya kai 328 bayan da suka warke daga cutar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China