Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya nemi a samar da rigakafi da maganin cutar numfashi
2020-01-31 16:41:51        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar gaggauta samar da rigakafi da maganin cutar numfashi da kwayar cutar Corona ke haifarwa.

Li Keqiang, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban tawagar kwamitin kan hanyoyin kariya da takaita yaduwar cutar numfashin, ya yi jawabin ne yayin da yake rangadi a cibiyar takaita yaduwar cuttuttuka ta kasar Sin.

Yayin rangadin, firaministan ya saurari bayanai game da binciken kimiyya kan matakan kariya da takaita yaduwar cutar, tare da ra'ayoyin kwararru kan batun.

Ya ce ya kamata cibiyoyin takaita yaduwar cututtuka su gaggauta gano asalin cutar da kuma yadda take yaduwa, tare da gudanar da bincike kan samar da rigakafi da fasahohin da za su taimaka wajen ganowa cutar da kula da masu dauke da ita.

Da yake bayyana yanayin a matsayin mai sarkakiya, Li Keqiang, ya yi fatan kwararru za su karfafa bincike da nazarin cutar da gano sabon yanayinta domin taimakawa wajen dakileta.

Ya kuma bukaci a tabbatar da fitar da bayanai na gaskiya kan cutar yayin da ake yayata hanyoyin kariya na kimiyya.

Har ila yau, firaministan, ya bayyana cewa muhimmiyar hanyar cin nasara kan cutar ita ce, inganta hanyoyin ba da kulawa da rage yawan mace-macen da take haifarwa, yana mai cewa, ingantattun rigakafi da magunguna su ne za su magance annobar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China