Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Muna da karfin tsayar da yaduwar cutar numfashi a Sin, in ji hukumar kiwon lafiyar kasar
2020-01-31 16:06:45        cri
A safiyar yau Jumma'a, babban darektan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ayyana cutar numfashi da ta bulla a kasar Sin a matsayin "harkar kiwon lafiya ta gaggawa dake janyo hankulan kasa da kasa", kuma ya jaddada cewa, babu bukata daukar matakan hana yawon shakatawa a kasar Sin da kuma daina yin ciniki da kasar Sin. Sa'an nan, hukumar kiwon lafiyar kasar Sin ta bayyana a yau cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali matuka kan hana yaduwar cutar da kuma ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar, a halin yanzu, kasar Sin ta dauki muhimman matakai wajen hana yaduwar cutar. A don haka, kasar Sin tana imanin cewa, tana da karfin dakile yaduwar cutar da kuma kawar da cutar baki daya a duk fadin kasar.

Kafin haka, Tedros Ghebreyesus ya yaba matuka kan yadda kasar Sin take aiwatar da ayyukan hana yaduwar cutar, kuma ya yi imanin cewa, kasar Sin za ta cimma nasarar yaki da cutar.

A yau Jumma'a, hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta bayyana fatan cewa, gamayyar kasa da kasa za su baiwa kasar Sin goyon baya wajen aiwatar da ayyukan hana yaduwar cutar numfashin da ta bulla a kasar, da kuma yin hadin gwiwa da kasar bisa "dokar kiwon lafiya ta kasa da kasa" da shawarar WHO wajen hana yaduwar cutar a matakin shiyya da ma duniya baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China