Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sin ta yi shatar jiragen sama domin dawo da mazauna lardin Hubei 310 daga ketare
2020-02-01 16:21:59        cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin tare da wasu ofisoshin jakadancin Sin da ke ketare, sun hada hannu wajen shatar jiragen sama guda uku domin dawo da mazauna lardin Hubei 310 daga kasashen Thailand da Malaysia da ma Japan. Kuma a daren jiya, rukunin farko da ya hada da mazaunan 199, sun sauka a filin jiragen sama na Tianhe da ke birnin Wuhan, hedkwatar lardin Hubei.

Rahotanni sun ce, kamfanin sufurin jiragen sama na Xiamen ne ke kula da wannan aiki. Har ila yau, jiragen sama biyu sun sauka a birnin Hunan da karfe 8 da minti 53, da ma karfe 10 da minti 32, dukkansu a daren jiya. Bisa ka'ida, bayan binciken yanayin zafin jiki fasinjoji, a kan bar masu lafiya su sauka, yayin da za a killace wadanda ke da alamar zazzabi. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China