![]() |
|
2020-01-20 15:19:18 cri |
Shekarar 2020 shekara ta karshe a aikin kawar da kangin talauci da kasar Sin ke gudanarwa, kuma gwamnatin kasar na shirin dauka matakan da suka dace, don magance matsalolin da yankunan dake fama da matukar talauci ke fuskantar, don magance mutanen da suka fitar daga kangin talauci su sake komawa cikin sa.
Direktan ofishin tallafawa aikin yaki da talauci na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Liu Yongfu ya bayyana cewa, ya kamata a tabbatar da makasudin kawar da kangin talauci a shekarar 2020, da habaka sha'anin tallafawa matalauta, da kawar da talauci ta hanyar samar da guraben aikin yi, da dai sauran ayyukan kawar da talauci. Ta yadda za a fitar da sauran mutane na gundumomi da suke fama da kangin talauci, da ba da tabbaci ga zaman rayuwar matalauta na musamman.
An ce, yawan matalauta ya ragu zuwa kimanin miliyan 6 a karshen shekarar 2019, daga miliyan 98.99 a karshen shekarar 2012. Makasudin Sin a wannan fanni shi ne fitar da dukkanin matalauta daga kangin talauci a kauyukan kasar Sin kafin karshen shekarar 2020. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China